Shar’anta yin jahadi abin nufi da shi na karan kansa ne, ko kuma shi kofa ne daga cikin kofofin wasila.
Tambaya
Shin shar’anta yin jahadi abin nufi da shi na karan kansa ne, ko kuma shi kofa ne daga cikin kofofin na wasila?
Amsa
Shar’anta jahadi bai zamo domin karan kansa ba, dai an shar’anta shi ne a matsayin wata hanya daga cikin hanyoyin hana zalunci da ta’addanci akan al’umma, shin wannan ta’addancin da ake yunkurin yi wa wannan al’ummar saboda addininta ne, ko domin kwashe mata dukiya, da arzikinta, saboda haka muke samu a cikin mafi yawan ayoyin da suka yi magana akan shar’anta jahadi akwai ambaton dalilin da ya sanya aka shar’anta yin shi jahadin, daga cikin akwai fadin Allah Madaukakin Sarki: (Ku yaki mushirikai gaba dayansu kamar yanda suke yakarku gaba dayansu) [At-tauba: 36], dalilin umurni da yaki a wannan ayar shi ne mayar da martani akan mai ta’addanci kwatankwacin ta’addancin da ya yi, mu kaddara cewa mushirikai ba su yi ta’addanci akan Musulmai ba a lokacin Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), to fa da ba a yi wa Musulmai umurnin su yi jahadi ba, saboda shi jahadin hanya ce ta kawar da zalunci, to zaluncin bai auku ba, da haka ne za mu fahimci cewa shi ma’anar jahadi shi ne wajabcin samuwar abin da zai aukar da shi, sabanin kawar da zalunci da tsayar da adalci, su kuwa wajibi ne da ake nufin aukuwarsu a karan kansu, to wannan ya saba wa fahimtar masu tsattsauran ra’ayi wadanda suke ganin lallai jahadi wajibi ne na karan kansa wanda ake nufin aukuwarsa bisa manufarsa, daga haka za mu fahimci cewa shi Musulmi - a nasu tunanin – dole ya kasance cikin shirin yaki a kowani lokaci.