Bayar da kyautar gashi ko suma ga kananan yara masu fama da cutar kansa.
Tambaya
Shin ya halatta mutum ya bayar da kyautar gashi / sumar kansa ga asibitin cutar kansar kananan yara; da nufin a yi hular gashi da wadannan kananan yaran za su rinka sanyawa?
Amsa
Ya halatta mutum ya yi kyauta da wani sashe na gashi/ sumar kansa ga asibitin cutar kansa na kananan yara, da niyyar sana’anta hular gashi da ake sanyawa kananan yaran da suka rasa gashin kawunansu sakamakon amfani da sinadarin kimiyya a maganin da ake yi masu, saboda hakan zai tabbatar da wata muhimmiyar maslaha da shari’a take la’akari da ita, mai bayar da wannan kyautar a wannan lokacin yana da lada mai girma a wurin Allah mai girma da buwaya; saboda ya bayar da gudummuwa wajen rage damuwa da radadin da kananan yara da gashinsu ya zube sakamakon haka, bugu da kari kuma ya sanyaya masu zukatansu, wannan ba shi da dangantaka da masu Karin gashi, sannan kuma su kananan yara ba a daura masu yin haka ba, tunda ba su balaga ba.