Wasannin bidiyo da suke koya tashin hankali ga kananan yara
Tambaya
Mene ne hukuncin wasannin bidiyo da suke koya tashin hankali ga kananan yara?
Amsa
A cikin kayayyakin wasanni da suke amfani da lantarki, ko kwamfuta akwai masu amfani, akwai kuma masu cutarwa; masu amfanin halal ne, masu cutarwar kuma haramun ne.
Za su zama halal: idan ba su dauke da wani abu da aka haramta, su kuma zama sun yi daidai da shekarun wadanda za su yi wasa da su, ya kuma zama suna da amfani wajen kara kaifin basira da bude kwakwalwa, ko idan suka kasance suna samar da hutu ga rai, da sharadin kada ya zamana suna kunshe da abin da shari’a ta haramta, Kaman caca da sauransu, ya kuma zamana a samar da su ne akan ma’auni na tarbiyya da ake bi wajen irin yanda yara za su yi ta’amuli da wadannan wasannin.
Za su kuma zama haramun ne : idan suna cikin abubuwan da aka hana; saboda hatsarin da suke da shi akan daidaikun mutane, ko akan al’umma, ko kuma ya zama suna kunshe da abubuwan da aka haramta, irinsu: caca, ko akwai hotuna ko bidiyoyin batsa, ko suna kunshe da abin da yake nuna rashin muhimmancin ran dan Adam, ko kuma su na jawo tashin hankali, ko wulakanta abubuwa masu tsarki, ko kuma ya zama suna tallata munanan abubuwan da suke bata zukatan kananan yara da dabi’unsu, ko wadanda za su sanya su zama masu kawo tashin hankali da zalunci.