Wasannin bidiyo na fadace- fadacen ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Wasannin bidiyo na fadace- fadacen kananan yara

Tambaya

Mene ne hukuncin wasannin bidiyo na fadace- fadacen kananan yara?

Amsa

Wasannin bidiyo akwai masu amfani, akwai kuma masu cutarwa, masu amfanin sun halatta, masu kuma cutar sun haramta.

Za su zama halal ne: idan babu abubuwan da aka haramta a cikinsu, ya kuma zama sun dace da marhalan shekarun yaran da za su yi wasa da su, ya kuma zama suna da amfanin da yake taimakawa wajen samun kwarewa, da karin fahimtar kwakwalwa, ko kuma ya zama suna sanya nishadi, da sharadin kada ya zama suna kunshe da abubuwan da shari’a ta haramta irinsu: caca da sauransu, ya kuma zama an samar da su akan wani tsari na tarbiyya da ake bi wajen ta’amuli da kananan yara wajen gudanar da ire- iren wadannan wasanni.

Za kuma su zama haramun ne: idan an hana; saboda hatsarin da take kunshe da shi akan daidaikun mutane, ko akan al’umma, ko kuma yana zama tana kunshe da abin da yake haramun ne kaman caca, ko kallon batsa, ko tana kunshe da abubuwan da suke nuna rashin muhimmancin jinin dan Adam, ko kira zuwa ga fadace- fadace da tashin hankali, ko suna tozarta wuraren ibada, ko kuma suna tallat munanan fahimta masu lalata zukatan kananan yara da dabi’unsu, ko tana sanya wa su zama mafadata masu zaluntar mutane.

Share this:

Related Fatwas