Kaffarar rantsuwa
Tambaya
Mene ne gwargwadon kaffarar rantsuwa? Shin za a iya fitar da shi da kima?
Amsa
Ana yin kaffarar rantsuwar gamusi ne, watau rantsuwar da mutum ya yi sannan ya saba, shi kuwa lagawu ba a yi mata kaffara.
Kaffarar rantsuwa ita ce: ciyar da miskinai guda goma, ko tufatar da su, wanda kuma bai sami dam aba sai ya yi azumin kwanaki uku, Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Allah mai girma ba zai yi maku ukuba sakamakon rantsuwar da ba ku kudurce ma’anarta a cikin zukatanku ba, zai yi maku ukuba ne kawai saboda warware rantsuwar da kuka kudurce, kuma aka kulla alkawari da su, idan kun warware ranstuwar da kuka kulla, to dole ne ku aikata abin da zai zamo sanadiyyar yi maku gafara a matsayin kaffara ga rantsuwar, wannan abu kuwa shi ne; ku ciyar da talakawa goma da irin abincin da aka saba da shi, irin wanda kuke ciyar da kawunanku da makusantanku da suke karkashin kulawarku a rana daya, ba tare da ɓarna ko koro ba.. Ko kuma ku tufatar da talakawa goma da irin tufafin da aka saba da shi, ko kuma ku ‘yanta dan Adam daga bauta. Idan wanda ya yi rantsuwar bai sami daman yin ko daya daga cikin wadannan abubuwa da aka ambata ba, to dole ne ya yi Azumin kwanaki uku. Ana gafarta zunubin rantsuwar da aka warware bayan an yi ta da niyya ne idan aka aikata daya daga cikin wadannan abubuwa, ku kiyaye rantsuwarku kada ku yi rantsuwa a wurin da bai kamata ba, kada kuma ku bar aikata abin da za a gafarta maku idan kun warware ta, lallai da irin wannan bayani ne Allah Madaukakin Sarki yake yi maku sharhi game da hukunce-hukuncensa, domin ku gode akan ni’imoninsa da ya sanar da ku, ku kuma bayar da hakkokinsu kaman yanda suka dace) [al- Ma’ida: 89].
An kimanta kaffarar rantsuwa ne da sa’i daya na galibin abincin mutanen gari, kaman alkama, ko shinkafa, za a bai wa kowane daya daga cikin miskinai goma, kaman yanda yake a mazhabar Hanafiyya, ma’aunin sa’i na alkama kusan 2.500 kilogram kenan, game da shinkafa dan Misra kuwa ya kai 2.750 kilogram. Mazhabar Shafi’iyya kuma sun tafi akan cewa abin da ya wajaba shi ne mudu daya na galibin abincin mutanen gari, shi kuwa mudu daidai yake da kasha daya cikin hudu na sa’i daya, daidai kuma yake da gram 510 ga kowane miskini guda daya.
Wanda ba zai iya fitarwa daidai da mazhabar Hanafiyya ba, zai iya fitarwa daidai da mazhabar Shafi’iyya. Ya halatta a fitar da shinkafa ko alkama, haka ma ya halatta a fitar da kimansu ga talakawa, watau gwargwadon abin da zai ciyar da na abincin rana a kaffarar azumi, amma za a buga shi sau goma. Allah shi ne masani.