Rudar da mai sallah
Tambaya
Mene ne hukuncin rudar da mai sallah a lokacin da yake sallah, kaman a sanya shi dariya da makamantar haka?
Amsa
Rudar da mai sallah a lokacin da yake sallarsa ta hanyar sanya shi dariya, ko makamancin haka haramun ne, duk wanda ya aikata haka ya yi laifi.
Sallah ginshiki ne na addini, tana da girma gami da alfarma; ita ce ganawar da take kasancewa tsakanin bawa da Ubangijinsa mai girma da daukaka, dole ne bawa ya kasance cikin tsoron Allah, wanda da shi ne wannan ganawar take tabbata; saboda ya zama cikin wadanda Allah Madaukakin Sarki ya yi Magana akansu a inda yake cewa: (Lallai muminai sun sami babban rabo, su ne wadanda suke sanya tsoron Allah a cikin sallar da suke yi) [al- Muminuna: 1- 2]. Daga nan ne addinin Musulunci ya hana duk wani abu da zai rudar da mai sallah ya fitar da shi cikin yanayi na natsuwa da tsoron Allah, shin a lokacin da yake cikin sallah ne, ko bayan ya gama, sam bai halatta Musulmi ya keta alfarmar sallah ta hanyar sanya masu yi dariya, ko makamancin haka ba, saboda babban zunubin da yake cikin yin haka. Malamai masana fiqihu ba su bambance tsakanin kasancewar abin da zai sanya dariya, ko ya kawo rudu ga mai sallah ya zama abu ne na biyayya da da’a, ko kuma ya zama na sabo, inda suka bayyana haramcin yin haka idan ya zama ta hanyar aikin biyayya da da’a ne, saboda haka haramcin aikata haka da niyyar bai wa mai sallah dariya ya fi tsanani.