Fitar da zakkah
Tambaya
Shin ya halasta a fitar da zakka kashi-kashi har na tsawon shekara?
Amsa
Ya halasta ga mai tambaya a shari’ance ya fitar da zakkah kashi-kashi har na tsawon shekara guda bayan wucewar shekara akan dukiyar da aka fitar mata da zakkah, wanda ya kai nisabi zuwa ga wanda ya san cewa sun cancanta a kowani wata, tare da kiyaye ganin bai wuce shekarar zuwa wata ba, face har sai ya kamala fitarwa.