Addu’ar arba’in da na shekara
Tambaya
Mene ne hukuncin zaman arba’in da na shekara don tunawa da mamaci?
Amsa
Jamhur din malamai masana fikihu sun tafi akan cewa “mudda” wato lokacin zama a yi ta’aziyya shi ne kwanaki uku kawai, bayan wadannan kwanakin yin ta’aziyya makaruhi ne, sai dai ga wanda ba ya nan ne daga baya ya dawo, ko ga wanda bai san labarin rasuwar ba sai bayan wucewar wannan lokaci; saboda yin haka maimaita bakin ciki ne, da kuma daura wa iyalan mamaci nauyi.
Sam shari’a ba ta hana a yi taro a gabatar da wani aiki na gari a sadaukar da ladan haka ga mamaci ba; Kaman ciyar da abinci, da karatun Alkur’ani; shin a bayan kwanaki arba’in ne ko kuma bayan shekara.