Iddar wadda mijinta ya rasu ya barta
Tambaya
Mene ne iddar matar da mijinta ya rasu ya barta? Shin ya halatta ta fita a lokacin da take idda?
Amsa
Iddar matar da mijinta ya rasu ya barta shi ne watanni hudu da kwana goma, a lissafin kamariyya (Hijira); saboda ayar da Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Su kuwa wadanda suka rasu daga cikinku suka bar mata, za su tsahirta ga barin yin aure har na tsawon watanni hudu da kwanaki goma) [al- Bakra: 234].
Ya halatta ta fita daga gidan aurenta a yini, tare da la’akari da ta rika kwana a gidan aurenta a duka lokacin iddarta.
Allah Madaukakin Sarki shi ne masani.