Halascin yabo da bege

Egypt's Dar Al-Ifta

Halascin yabo da bege

Tambaya

Menene hukuncin yabon Annabi Sallahu Alaihi wa Alihi wa sallam da sauran nau’ukan bege da wakoki na addini?

Amsa

Daga cikin mafi girma da daukakan tafarki da bawa zai iya bayyana matukar son sa ga Allah Mai girma, da Manzonsa Mai girma shi ne bayyana : yabo da bege, domin kuwa su abubuwa ne da ke zama dalilai na nuna soyayya, da tabbatar da gaskiyar soyayyar, idan mutum yana son abu ya kan yawaita ambatonsa da yabonsa, domin abin da harshe ke ambatawa yana nuni ne kan abin da zuciya ke so, ko wani abu yakan kara samun dagomashi ta hanyar yabo, amma banda yabon Allah da begen Annabi S.A.W. domin wanda ke yabon su shike samun daukaka, a hakikanin gaskiya ba wanda ya dace da yabo kamar Allah Ta’ala da Manzonsa Mai girma S.A.W.

A cikin hadisin Al’aswad bin Sare’e Allah ya kara masa yarda ya ce: “ Nace ya Manzon Allah “ Na yabi Allah da wani irin yabo, sai ya ce: (Kawo muji bayyana yanda ka yabi Mai girma da Buwaya) {Imam Ahmad ne ya ruwaito}.

Share this:

Related Fatwas