Falalar ciyar da abinci.
Tambaya
Mene ne falalar ciyar da abinci a Musulunci?
Amsa
Nassosi sun zo daga Alkur’ani Mai girma da Sunna Mai tsarki kan cewa shi ciyar da abinci yana daga cikin mafi soyuwar ayyuka zuwa ga Allah Ta’ala, kuma hakan na daga cikin abubuwan bukata domin samun karbuwa, har hakane ma yasa Allah Ta’ala ya sanya hakan daga cikin dalilan rabauta da shiga Aljanna, Allah Ta’ala ya yabi bayinsa muminai, inda yake cewa: (Suna ciyar da abinci tare da tsanin bukatar abinci), {Al’Insan:8}.
An karbo daga Abdullahi bin Amru Allah ya yarda da su: Lallai wani mutum ya tambayi Annabi SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam cewa: Mene ne yafi alheri a cikin Musulunci? Sai ya ce: (Ka ciyar da abinci, ka yada sallama ga wanda ka sani da wanda baka sani ba). An yi ittifaki akansa.
An karbo daga Aliyu bin Abi Dalib Allah ya yarda dasu ya ce: Annabi SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam ya ce: (Lallai a cikin Aljanna akwai wasu dakuna da ake iya ganin cikinsu daga wajensu, ake iya ganin wajensu daga cikinsu), sai wani balaraben kauye ya ce: wannan gidan na waye ya Manzon Allah? Sai ya ce: (Na wanda yake kyautata zancensa ne, yake ciyar da abinci, ya dawwama yin azumi, ya kuma yi sallah cikin dare a lokacin da mutane suke barci) Ahmad.