Kare martaban kasa
Tambaya
Mene ne alamomin da musulunci ya yi kira a kansu wurin kare martabar kasa? Kuma mene ne dalilin haka?
Amsa
Shari’ar musulunci ta yi kira zuwa ga samarwa kasashe aminci (zaman lafiya), alamomin da ke bayyana haka shi ne sanya son kasa a zukatan mutane, domin hakan wani abu ne na halitta dake bubbugowa daga jikin mutum, ta hanyar damfara da kasarsa da kuma nuna kauna zuwa ga wurin da ya taso a cikinsa ya kasance yana da abubuwan tarihi da ke wadanda ya taso tare da su, irin hakan ya bayyana cikin aikin Annabi S.A.W. inda soyayyarsa ga mahaifarsa ya kasance cikin dabi’unsa.
An karbo daga Anas bin Malik Allah ya kara masa yarda ya ce: (Annabi S.A.W. ya kasance idan ya dawo daga tafiya ya hango manyan hanyoyin Madina, ya kan sanya abin hawansa ya yi sauri, idan kuma dabba ce ya kan zunkuda ta don tayi sauri) Bukhari ne ya ruwaito.