Tauna wani abu kamar dabino a sanya...

Egypt's Dar Al-Ifta

Tauna wani abu kamar dabino a sanya a bakin jariri

Tambaya

Menene ma’anar a tauna wani abu a sanya cikin bakin jariri kuma mene ne hukuncinsa kuma ya akeyi?

Amsa

Abin da ake kira da nufi da “Tahneek” Shi ne dandaka wani abu ko taunawa kamar dabino ko zuma ko wani abu mai kama da haka a sanya a bakin jariri, malaman fikihu sun yi bayani a kan kasancewar hakan sunna ne kuma ana son yin hakan, dalilin haka kuwa shi ne yanda Annabi S.A.W. ya aikata, an karbo daga Abu Musa Al’Ash’ari Allah ya kara masa yarda ya ce: {An haifa mini yaro, sai nazo da shi wurin Annabi S.A.W. sai ya rada masa suna Ibrahim, sannan ya tauna masa dabino a bakinsa} “ Anyi ittfaki akansa” tare da jan hankali bisa kasancewar duk wanda zaiyi wannan aikin to ya zama masani ne kan hakan kuma kwararre, domin kar rashin kwarewar ya cutar da shi jaririn, sai hakan ya cutar ya lalata komai duk da zaton da yake yi na son yin gyara.   

Share this:

Related Fatwas