Ta’amuli da abu mai sanya maye domin magani.
Tambaya
Mene ne hukuncin ta’amuli da abu mai sanya maye da niyyar yin magani?
Amsa
Bai halasta ba a shari’ance ayi amfani da magani mai sanya maye da sunan neman waraka, sai dai fa idan likita ne wanda yake kwararre kuma amintacce shi bayar da wannan umurnin na yin amfani da magani mai sanya mayen, sannan kuma ya zama dole shi mare lafiyan ya kiyaye kada ya ketare adadin shan maganin kamar yanda likitan ya umurceshi da shi.