Kare jinin musulmai daga kwarara

Egypt's Dar Al-Ifta

Kare jinin musulmai daga kwarara

Tambaya

Shin aikata sabo ko raunin Imani na iya halasta jinin musulmi wanda ya furta Kalmar shahada ta (La’ilaha illallahu wa anna Sayyidna Muhammad rasulullah?) shin furta wannan Kalmar ta shahada kan zama 

Amsa

Malamai na farko da na karshe sun cimma matsaya akan kiran duk wanda yayi Kalmar shahada a matsayin musulmi, don haka jininsa da dukiyarsa da mutumcinsa ya haramta a zubar dasu, koda kuwa wanda ya kasance hakan mai sabo ne, hakika Annabi SallallaHu AlaiHi wasallam ya fadakar kan aikata laifuffuka da zunubai domin hakan yana da cikin lamuran Imani kamar yanda yazo cikin Hadisin da Abu Dauda ya ruwaito daga Anas bin Malik inda ya ce : Manzon SallallaHu AlaiHi wasallam  ya ce : (Abubuwa uku suna daga cikin tushen Imani: kamewa daga cutar da wanda ya ce La’ilaha Illallah, domin ba mu kafirtashi bisa wani zunubi da ya aikata, hakanan ba mu fitar da shi  daga musulunci ba saboda ya aikata laifi) Abu Dauda.

Tare da muhimmancin da ke tare da aikata kyakkyawan aiki da alfanunsa, tare da rashin raina abinda aka aikata a lokacin da ya gabata.

Abinda ke zaman a gaskiya shine kamewa daga cutar da wadanda suka yi kalmar shahada ba tare da bukatar wasu abubuwan sabanin haka ba domin tsira da kawunansu daga kekketa huruminsu da zubar da jininsu, Annabi SallallaHu AlaiHi wasallam bai shardanta wani abu na shiga musulunci ba face da yin furuci da Kalmar shahada, ya kasance yana cewa (Duk wanda yayi sallah irin tamu, ya kuma fuskanci alkiblarmu, sannan ya ci yankanmu, to fa wannan shine cikkakken musulmi wanda ke da wuyayen Allah da na Manzonsa akansa, don haka kada ku tozarta Allah a cikin wuyayensa wurin ketare iyaka) Bukhari ne ya fitar da wannan Hadisin,

Share this:

Related Fatwas