Kungiyoyin kafirta Musulmai sun fita daban
Tambaya
Sau da yawa muna ganin kungiyoyin da suke kafirta Musulmai suna nesantar rayuwa da take dabi’a ce ta al’ummomi, shin a fagen sanya tufafi ne, ko a tsarin rayuwa, ko tunani, mene ne ya sanya haka?
Amsa
Kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi da na ‘yan ta’adda, da masu goya masu baya, da wadanda suke ba su tallafi dukansu sun yi imani da abin da za mu iya kiransa da suna “Hasashen kwaikwayon abin da ya zo”, ko bin da wasu suke kira da shigar burtu, wanda hakan yana nufin kirkirar wani yanayi da ya yi kama da yanayin da nassoshin shari’a suka zo da shi; ta yanda za a yi da’awar cewa wannan kungiyar ita ce ake nufi da wadannan nassoshin, ko za ta shiga cikinsu.
Inda wadannan kungiyoyin suke buya shi ne nemo nassoshin da suka zo a wasu yanayi mabambanta, ko wasu nassoshi da suke Magana akan tarihi, su kuma su sake kwaikwayon wannan yanayi akan cewa su ne ake nufi a wadannan nassoshin, akwai misalai masu yawa game da haka, wadanda suka ambaci wasu sifofi da aka ambata akan wani yanayi na gaibi da Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya bayar da labara, bayan Allah ya sanar da shi a matsayinsa na annbi.
Alal misali: bayyana bakaken tutoci a kasashen Musulmai, saboda masu sun suna neman su kwaikwayi abin da ya zo daga (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) na cewa: (Idan kun ga bakaken tutoci sun zo daga Hurasan, to ku dunguma ku je wurinsu; domin a cikinsu akwai halifar Allah al- Mahdi).
Sai suka kwaikwayi wannan Hadisin, suka bayyana wa mutane da bakaken tutoci, kawai saboda su tara mutane, kai k ace su ne ake nufi da wannan Hadisi a aikace. Haka a tsawon tarihi aka yi ta samun kungiyoyi na mutane da suke daukan tutoci bakake saboda su kwaikwayi wadannan nassoshi da suka zo.
A wannan zamanin z aka sami wasu daga cikin kungiyoyin da suke riya yin jihadi suna zartar da wadannan Hadisai da suka zo a matsayin labarai, su kuma su mayar da su hukunce- hukunce na shari’a da wajibi ne a aiwatar da su.