Alaka tsakanin “yada karya domin ts...

Egypt's Dar Al-Ifta

Alaka tsakanin “yada karya domin tsarotar da mutane” wato (Irjafi) da kuma jihadi

Tambaya

Mene ne hakikanin ma’anar Irjafi? Kuma mene ne alakarsa da jihadi wurin daukaka Kalmar Allah?

Amsa

Amsa :

Lallai abinda kungiyoyin ‘yan ta’adda ke yadawa - wanda ke lullube da rigar musulunci da ma’anoninsa madaukaka-  kan cewa abinda suke aikatawa na cin zarafi da kekketa hurumomi da zubar da jini da aka hana cewa shine jihadi, to wannan kuskure ne sakamakon mummunar fahimtarsu akan lamuran addini, saboda abinda suke aikatawa sunansa “ yada karya domin tsarotar da mutane” wanda Allah Ta’ala ya ambata a cikin zancensa: {Idan munafukai da wadanda suke da ciwo a cikin zukatansu da  masu yada karya domin tsarotar da mutane ba su hanu daga abubuwan da suke aikatawa ba to lallai za mu fallasa maka su sannan ba za su sake makwaftakarka ba sai dan kadan daga cikinsu* su ababen la’anta ne a duk inda aka same su akama su a akashe su kisha mai muni* irin hakan dai sunnar Allah ce a cikin bayinsa da suka gabata kuma ba zaka taba samun wannan sunnar ta Allah ta caccanza ba} Al’Azhab 60 – 62, don haka Kalmar “Irjafi” tana da mummunar ma’ana wanda ke kunshe da tayar da fitinu da tashin hankali da kuma damuwa wanda ke haifar da halasta jini da dukiya a karkashin kiraye kiraye mabanbanta, daga cikin haka akwai: kafirta hukumomi da kasashe ko wasu kungiyoyi ayyanannu a cikin mutane, daga ciki akwai halasta jinin musulmai karkashin ikirarin yin umurni da kyakkyawan aiki da kuma hani zuwa ga mummunan aiki, ko kuma zubar da jinin wadanda ba musulmai ba a kasashensu ko kuma wadanda suka shigo cikin kasashen musulmai daga cikinsu bisa ikirarin cewa kasashen su wadanda ba musulmai ba suna yakar musulunci, tare wasu ayyukan da suke aikatawa na salon tsoratarwa da shedan ke zuga su da aikatawa, wanda wani sashe na dalilin wannan aikin na su shi ya haifar da bayyanar Hawarijawa a lokacin sahabbai da wanda suka zo bayansu, haka akwai kamanceceniya da suke fakewa da shi kan aikata barna a bayan kasa da kuma zubar da jinin da aka haramta.

Share this:

Related Fatwas