Yin amfani da kayan jingina ga wand...

Egypt's Dar Al-Ifta

Yin amfani da kayan jingina ga wanda aka jinginarwa da kaya.

Tambaya

Mene ne hukuncin wanda aka jinginarwa da abu, sannan ya yi amfani da abin jinginar?

Amsa

Bai halasta ba a shari’ance mai karban jingina na kaya ya yi amfani da kayan jinginan, sai dai fa idan ya biyan kudin amfani da kayan, koda kuwa kudin kimar kayan jinginar ya bayar, idan ba haka ba to wannan yana daga cikin cin kayan  mutane da barna, kuma hakika Allah Ta’ala ya yi hani akan hakan a cikin fadinsa: (Ya ku wadanda ku ka yi imani kar ku ci dukiyarku da take tsakaninku da barna sai dai fa idan a halin kasuwanci ne wanda yake gudana bisa yardanku kuma kar ku kashe kawunanku domin lallai Allah ya kasance mai tausayi ne gareku Duk wanda ya aikata hakan a bisa keta da zalunci da sannu zamu shigar da shi wata irin wuta Kuma irin wannan a wuin Allah abu ne mai sauki) {Nisa’i: 29-30}, saboda shi irin wannan yana daga cikin babi ne na bashi wanda yake kaiwa ga samun amfani, wato dai riba kenan.

Share this:

Related Fatwas