Kamanceceniyar da ke cikin Al’kur’ani a wurin kungiyoyin ‘yan ta’adda
Tambaya
Ta yaya masu tsattsauran ra’ayi ke mu’amala da kamanceceniyar ayoyin Al’kur’ani Mai girma.
Amsa
Hakika masu son zuciya da batattun mutune sun dauki lamarin kamantattun abubuwa dake cikin Al’Kur’ani domin su batawa mutane akidarsu, sai suka kasance suna yin amfani da wannan salon ne domin jawo ra’ayin mabiya da magoya baya, sai suka canza ma’anonin Al’Kur’ani Mai girma domin tayar da fitina da kuma neman abubuwan duniya na jin dadi, hakika Allah Ta’ala ya sani cewa a cikin wannan al’umma za asamu wasu mutane da suke ikirarin samuwar kamanceceniya a cikin Al’Kur’ani Mai girma wanda muminai ke tabbatar da samuwarsu, sai Allah Subhanahu wa Ta’ala ya ce : (Amma wadanda suke tare da bata acikin zukatansu to suna bin kamanceceniyar ne domin neman fitina da kuma yin tawili a ciki* kuma ba wanda yasan tawilin da ke cikin Al’Kur’ani sai Allah* Amma su wanda suka samu rabauta na tabbata cikin ilimi sukan ce munyi Imani da shi domin duka daga Ubangijinmu ne* babu mai wa’azantuwa da irin haka face masu hankali) {Ali Imran: 7}, sai masu munanan tunani suka dauki sashen kamanceceniyar dake cikin Al’Kur’ani suka sanya shi ya zama hanyarsu da dalilinsu da kuma jagoransu zuwa ga kowani hukunci na addini da na duniya, inda suke tsinkayan ayyukansu daga irin wannan tunanin a cikin mu’amalarsu da kuma dukkan halayensu domin su kafa hujjar yin barnansu da kuma kawata laifuffukansu.
Daga cikin misalai akan haka, shine inda Hawarijawa suke kafa hujja wurin lalata duk wani hukunci na daban bisa fadin Allah Subhanahu wa Ta’ala: (Lallai babu wani hukunci sai na Allah) {Al’An’am:57}. Ma’anar dake cikin wannan ayar ingantacce ne a cikin jumla, sai dai fa a bayyane akwai bukatar yin bayani, saboda haka ne Aliyu bin Abi Dalib – Allah ya kara masa yarda - ya yi musu raddi inda ya ce musu: “Kalmar gaskiya aka fadi amma barna ake nufi da ita”