Mace ta karanta Alkur’ani da kayan zaman gida
Tambaya
Mene ne hukuncin mace ta karanta Alkur’ani da kayan zaman gida?
Amsa
Ana son Musulmi idan zai karanta Alkur’ani ya zama ya suturta al’aurarsa, ya kuma kasance a cikin yanayi mai kyau, mace ta karanta Alkur’ani da kayan zaman gida a jikinta ba tare da ta sanya hijabi ba abu ne da ya halatta a shari’a; saboda rufa kai a lokacin karatun Alkur’ani ba wajibi ba ne, amma idan ta rufe a babin cikakken ladabi wa littafin Allah, to hakan ya fi falala.