Manufofin ayoyin Al’kur’ani a wurin...

Egypt's Dar Al-Ifta

Manufofin ayoyin Al’kur’ani a wurin ‘yan ta’adda.

Tambaya

Shin ma’abota tsattsauran ra’ayi suna lura da ma’anonin Al’kur’ani Maigirma da manufofinsa kuwa?

Amsa

Masu tsattsauran ra’ayi suna tsinkaya zuwa ga ayoyin Al’kur’ani Maigirma bisa son ransu, inda suke caccanza ma’anoninsu ba sa kiyaye manufofinsu, sai ka gansu suna sanya ma’anar ayoyin da suka sauka akan wadanda ba musulmai ba akan musulmai, to fa irin wannan yana haifar da musu da kaucewa daga kan tafarkin Sunnar Annabta mai tsarki, kamar yanda hakan ke haifar da canzawar ma’auni da fahimta inda hakan ya sanya mummunar aiki ya zama kyakkyawa, sannan abinda ke zama mai kyau zuwa mummuna, sai suka kasance suna sanyawa mutane shakku tare da jefa su a cikin rudani na tunani, Annabi SallallaHu AlaiHi wasallam ya ce:  (Lallai wani tsatso zai fito daga cikin wadannan mutanen da za su rinka karanta Littafin Allah da murya mai dadi amma ba ya wuce makogwaronsu, suna shiga cikin addini su fice – da sauri – tamkar dai yanda kibiya ke huda abin farauta ya fice. Sai ya ce: Amma ina zaton ya ce ne: Idan har na riske su to lallai sai na kashe su irin kisan da aka yiwa samudawa){Muslim}. A zancensa na cewa: “Suna karanta Al’Kur’ani amma ba ya wuce makogwaronsu” wato dai suna karanta shi, sai dai ba sa fahimtar ma’anoninsa da manufofinsa, da hakan sai suka fice daga tafarkin al’ummar musulmai, mai ya kai kyan abinda sashen magabata suka ce akan Hawarijawa: Sune fa aka ambata a cikin fadin Allah Ta’ala: (Shin ba ma baku labarin wadanda suke zama mafi asarar ayyuka ba* Wadanda ayyukansu suka lalace a rayuwar duniya amma suna raya cewa suna kyautata ayyukansu ne* To fa wadancan sune wadanda suka kafirce da ayoyin Ubangijinsu da kuma saduwa dashi da wannan ne yasa ayyukansu suka lalace to fa ba su da wani sakamako na aikinsu ranar alkiyama) {Al’Kahfi: 103 – 105}

Share this:

Related Fatwas