Sifofin da Annabi (SallalLahu alaiH...

Egypt's Dar Al-Ifta

Sifofin da Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya bambanta da kowa akansu

Tambaya

Yaya masu tsattsauran ra’ayi suke kallon falala da karamomin da Allah ya kebance Annabinsa da waliyyansa?

Amsa

A cikin ma’anonin da suka bambanta tsakanin ingantaccen hankalin Musulmai da hankalin masu kafirta Musulmai akwai mas’alar sifofin da Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya kebanta da su, da kuma abubuwan da Allah ya kebance salihai da waliyyai da sun a falala da karamomi, da abin da ya ginu akan haka na hukunce- hukunce; domin lallai rashin fahimta ko riskar falala da darajojin da Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya kebanta da su shi ne ya kai wadannan masu kafirta Musulmai zuwa ga kafirta wasu daga cikin Musulmai da suke tawassuli da Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) a wajen addu’a, inda a karshe suke kai wa zuwa ga yakarsu, haka abin yake ma cikin hakki wasu salihai da waliyyai da wasu Musulmai suka yi amannan cewa suka da falala gami da karamomi, kuma ziyararsu aiki ne na kwarai da ake kusantar Allah Madaukakin Sarki da ita. Jahiltar wadannan abubuwa shi ne yake kai wa zuwa ga kafirta Musulmai da yakarsu ba tare da hakki ba, saboda haka dole ne a fahimci abin da ake nufi da khasa’is din Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), a cikin manyan abubuwan da suke cikin ilmin Fikhu akwai bambanta tsakanin abubuwan da Allah ya kebanci Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) da su, da kuma abubuwan da suke shari’a ne ga al’umma, shin a farkon ba a yin kiyasi akansa.

Asali a cikin ayyukan da Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya aikata shi ne suna game kowa, kuma shari’a ce ga daukacin al’umma, babu abin da zai fita daga cikin wannan asalin sai abin da wani ingantaccen dalili ya nuna cewa ya fita daga ciki, saboda nassoshin shari’a sun saba neman Musulmai su yi koyi da shi.

A cikin nassoshin Alkur’ani da suka yi nuni zuwa ga haka akwai maganar Allah Madaukakin Sarki da yake cewa: (Lallai kuna da abin koyi mai kyau a cikin rayuwar Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), wannan koyin zai kasance ne ga wanda ya yi imani da Allah, ya kuma yi imani da ranar lahira, sannan ya ambaci Allah da yawa) [al- Ahzab: 21].

Share this:

Related Fatwas