Rangwamen Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) da lura da yanda mutane suke ji
Tambaya
Yaya Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yake la’akari da yanda mutane suke ji yake?
Amsa
Mu’amalar Musulmai da wadanda ba Musulmai ba an gina ta ne akan rangwame da rayuwar tare da kuma mutuntawa; domin shari’a ta bayar da umurnin a bayyana masu kyautatawa da rahama da adalci da ihsani, musamman tare da wadanda ake da bambanci da su a addini da akida, Allah Mai girma ya ce: (Allah bai hana ku yin mu’amala ta biyayya da adalci da wadanda ba su yake ku saboda addininku ba, ba kuma su fitar da ku daga gidajenku ba, ku yi masu adalci, lallai Allah yana son masu adalci) [al- Mumtahana: 8], sai dukansu suka rayu a cikin inuwar Musulunci, Musulmai suna mutunta akidu da al’adunsu.
Rangwame irin na Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya kai har sai da ya hana Musulmai zagin mamatan mushrikai bayan sun yi mutu, saboda a girmama ‘ya’yansu, da kuma rashin tayar masu da hankula; kaman yanda ya zo a maganar da (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya yi wa sahabbansa cewa: (Ga Ikramat Bn Abu Jahal nan zai zo a matsayin mumini da ya yi hijira, kada ku zagi mahaifinsa; domin lallai zagin mamaci yana cutar da wanda yake a raye, ba kuma ya zuwa ga mamacin) [al- Wakidiy a cikin al- Maghaziy].