Matsayin musulunci akan ra’ayi da z...

Egypt's Dar Al-Ifta

Matsayin musulunci akan ra’ayi da zafafawa a cikin addini

Tambaya

Mene ne matsayin musulunci akan tsattsauran ra’ayi da zafafawa a cikin addini?

Amsa

Ana kallon lamarin kalubalantar ayyukan ta’addanci a matsayin daya daga cikin lamura masu matukar muhimmanci wanda yake da hatsari mai girma, saboda hatsarin da yake tattare a hakan ya shafi matsalar tsaro da zamantakewar al’umma, hakanan alamomin hakan suna da yalwa da gurabu masu hatsari a cikin rayuwarmu ta yau da kullum.

Wanda hakan ya haifar da samuwar zuga a bayyane domin tayar da zaune tsaye, inda kafofin yada labaru da ake iya kallo ko ake sauraro ko ake karantawa suka taimaka wurin hakan, hakanan manhajin karatu a wasu kasashen shima ya taimaka sosai tare da gabatar da wasu karatuttuka da hudubobi na addini wanda suke karkatattu, hakanan wasu mazhabobi da shahararrun malaman addini mai tsanani sun taimaka wurin ruruta wutar samuwar tsattsauran ra’ayi, saboda irin tasirin da suke da shi ga wasu daidaikun mutane da kuma kungiyoyi saboda halayyarsu.

Yana daga cikin abubuwa masu muhimmanci anan mu karfafa cewa shi lamari na tsattsauran ra’ayi ba zai yiwu a takaice shi ga wasu mutane na daban ko a wani yanki ayyananne ba, daga cikin abun da za a iya lura da shi anan shi ne gungun sanannun mutane da aka sani da tsattsauran ra’ayi suna da alaka da kungiyoyin ta’addanci, sai dai fa a hakika shi tsattsauran ra’ayi yana yaduwa a tsakanin mutane ne masu yawa a cikin al’umma wanda hakan ba dole bane ya zama sifa ne ga wasu mutane na daban ba.

Hakika musulunci ya zo da koyarwa mai sassauci, ya kuma yi kira zuwa ga tsakatsakin lamura da daidaito a dukkanin lamura, don haka hakika manhajin musulunci - a koda yaushe – a tsaye yake wurin rangwame da karban bakon abu tare da barin tsattsauran ra’ayi da zafafawa, don haka ne ma musulunci ya kasancewa lamarin tsaurin ra’ayi da zafafawa a madakata karara, inda ya yi kira zuwa ga barinsa da nesantarsa da kuma kalubalantarsa.

Share this:

Related Fatwas