Matsayar musulunci bisa kasashen duniya.
Tambaya
Mene ne matsayar musulunci kan kasashen duniya a wannan lokacin? Kuma shin matsayar ya karkata ne zuwa ga adawa bisa dukkan abinda ba na musulunci ba?
Amsa
A halin da ake ciki yanzu a duniya na samuwar kungiyoyi da yarjejeniyoyi na kasa da kasa da kasashen musulmai sukayi tarayya wurin assasawa da kasancewa manbobi da tabbatar da ita kuma suka samu karbuwa daga malaman musulmai da cibiyoyin fikihu, duk wannan yanayin ya sanya kasashen duniya sun zama kasashen aminci da kira zuwa ga Allah da kuma alkawarin zaman lafiya, kuma a cikin haka akwai samun alfanu ga musulmai daidaikunsu da kungiyoyinsu, suna yin tafiya zuwa gabashin duniya da yammaci cikin tsanaki, hakika sashensu suna ma zaune ne a kasashen da ba a aiwatar da shari’ar musulunci a cikinsu, sai dai – Duk da hakan – suna gudanar da ibadansu cikin ‘yanci da walwala.
Hakika Annabi SallallHu AlaiHi wasallam ya tsananta bayani akan haramcin muzgunawa mu’ahidi, wato “kafirin amana” duk fa da rashin musuluntarsa, inda ya haramta zubar da jininsa da wawushe dukiyarsa, inda ya ce : (Ku saurara, duk wanda ya zalunci kafirin amana ko ya wulakantashi wurin dora masa nauyin da ba zai iya saukewa ba, ko ya amshi wani abu daga gareshi ba bisa son ransa ba, to nine abokin husumarsa ranar Alkiyama, ku saurara, duk wanda ya kashe kafirin amana wanda ke da wuyayen Allah da wuyayen Manzonsa to Allah ya haramta masa jin kamshin Aljanna, kuma akan iya tsinkayar kamshinta ne daka kilomita Saba’in), Baihaki.
Amma mas’alar kafirta mutane – shin ya kasance kan daidaikun mutane ne ko kasashe ko al’ummu – ya kamata a kiyaye hakan, baya halasta ayi hakan idan ba daga sashen malamai hakan ya fito ba, wadanda ke da masaniya akan lamura ko kuma wanda ke da hakkin bayar da fatawa, sai hakan ya kasance ta hanyar fitar da wani hukunci ne karkashin doka da alkali ya tabbatar, Al’imam ibn Hajar ya ce : “Ya kamata ga mai bayar da fatawa da ya yi kokarin kaucewa kafirtar da mutane gwargwadon ikonsa saboda hadarin dake tattare da hakan, tare da nesantar maimaituwar hakan musamman daga gamagarin mutane”.
Duk wanda ya musanta wannan lamarin ya kuma gurbatawa mutane rayuwarsu to fa ya fita daga tsarin musulunci da musulmai,