Kirkiran sabbin fahimtoci a fagen a...

Egypt's Dar Al-Ifta

Kirkiran sabbin fahimtoci a fagen addini.

Tambaya

Mene ne hatsarin da ke tattare da ayyukan da kungiyoyin ‘yan ta’adda ke aikatawa na samar da sabbin ma’anoni masu cike da kusakurai akan musulunci tare da yada hakan a tsakanin mutane a matsayin abubuwa sahihai? 

Amsa

Amsa:

Fahimtar abubuwa na kasancewa abu mafi kololuwa wurin tantance tunani da nazarurruka, saboda wadannan fahimtocin sun samu ne sakamakon kokari na kwakwalwa mai wanzuwa dake zama a jere har zuwa ga samar da ingantaccen tsari na (fahimtar) daga karshe wanda ke cike da hikima, wanda ke tabbatar da irin kai komon duk wani tunani,  tare da kokarin assasawa da gina duga-dugai na ilimi, to wannan shi ne yake baiwa lamarin ‘yanta fahimta muhimmanci na ilimi da tunani.

Idan har lamarin ‘yanta fahimtoci na gama gari da kunsassun abubuwa na bai daya suna da muhimmanci ta kowani fuska, to lallai hakan ya zama daya daga cikin lamura na dole musamman ga al’ummar musulmai, musamman bisa la’akari da halin da farfajiyar tunane-tunane ke kasancewa a duniyar musulunci sakamkon rashin samun tabbaci a wurin tantance tunani mai inganci ko akasinsa, wanda hakan wani yanayi ne da ba a saba ganinsa ba, idan har muka ce irin  wannan rashin tabbas din - na fahimta – da ake samu yanzu wata hanya ce ta rushe tsari da wayewar musulunci, to ba mu tsananta ba, saboda hakan yana tabo hakikanin lamari ne na musulunci daga can ciki, sannan kuma wannan rikicin na fahimtar yana haifar da tasgaro sosai a cikin lamuran musulunci.

Idan har muka bijiro da tambaya ta tunani ga masu da’awar tsaurin ra’ayi a karshen wannan lokaci, za mu ga a koda yaushe akwai yinkuri na farlanta wasu sabbin fahimta, wanda suke bayyanawa a kan “Tauhidi” da “Gidan musulunci” da kuma :Hakimiyya” da “Jihadi” da makamantar haka, domin irin wancan tsarin shi ke kamanta yanda ake son abubuwa su canza ko su kasance, ta fuskar batawa musulunci suna ta hanyar shigar da sabbin abubuwa, kai ba ma haka ba, wannan illarsa yana iya shafan dukkan shari’oin da aka saukar.

Share this:

Related Fatwas