Kiran sallah kafin asuba da rabin a...

Egypt's Dar Al-Ifta

Kiran sallah kafin asuba da rabin awa.

Tambaya

Mene ne hukuncin kiran sallah kafin asuba da rabin awa?

Amsa

Imam Bukhari da Muslim sun ruwaito a littafansu, daga hadisin Abdullahi bin Umar Allah ya yarda da su, daga Uwar muminai Aisha Allah ya kara mata yarda, daga Annabi SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam, yace:( Lallai Bilal yana kiran sallah a cikin dare, to ku yi ta cin abincinku, ku sha abin shan ku har sai Ibn Ummi Makhtum ya kira sallah tukuna), hakika jumhorin malamai da wannan hadisin suke ganin halascin yin kiran sallah kafin fitowar alfijir domin sanar da mutane kusantowar shigar lokaci, domin ma Imam Bukhari ya ware babi guda akan wannan lamarin a cikin littafinsa: (Babin kiran sallah kafin alfijir),  duk da cewa ya wajaba a kiyaye yanayin mutanen wuri da abinda suka saba, domin cewa dai a Musulunci babu cuta babu cutarwa, don haka sai a rinka komawa da lamura akan haka zuwa ga hukumomin da abin ya shafa, kada daidaikun mutane su rinka aiwatar da abinda zai haifar da rudani ga mutame, su na masu dogara da ijitihadinsu.   

Share this:

Related Fatwas