kafofin yada labaru na zamani.
Tambaya
Wani irin gudunmawa kafofin sadarwa na zamani suke bayarwa wurin yada tsattsauran ra’ayi da ta’addanci?
Amsa
Hakika intanet ya kasance wani irin dandali ne na baje kolin ayyukan ‘yan ta’adda, wanda suke gabatar da ayyukansu a kan wannan dandali, hakanan sukan yi amfani da shi wurin kalubalantar rashin nasarar da suka samu a karawarsu da jami’an tsaro, hakika Abu Mus’ab Al’sury ya yi tsokaci akan wannan batun a littafinsa mai suna (Da’awar gwagwarmaya ta musulunci), tun a farkon lamari, tare da yin kira kan samar da wasu hanyoyi na daban, inda ya bayyana a cikin littafinsa da aka ambata a baya – Bayan shan kaye wurin kasa samar da hanyar horar da magoya baya kai tsaye – tare da bayyana dalilan karkata zuwa ga “jihadin daidaikun mutane” wannan yazo ne bayan rashin samun nasara akan samar da kungiyoyin asiri sakamakon hare haren da kasa da kasa ke yawan kai musu, tare da gazawar kungoyoyin sirrika na iyawa da samarin al’umma wurin sanya su yaki da gwagwarmaya da wasu ayyukan na daban, kuma hakan na kasancewa ne ba tare da sanin daga ina suke ba a cikin kungiyoyinsu, yawaitan samun abokan gaba da saurin yaduwar manufofinsu a wurare daban daban wanda zai yi wuya a iya samunsu da kungiyoyinsu da cibiyoyinsu sanannu abu ne mai wuya, hakanan wuyan da ke tare da yin fito na fito da wanda yake a boye a wurare marasa tabbaci a matsayin abokan gaba wani abu mai wuyan gaske, wannan shi ya haifar da amfani da tsarin kai hare hare ta sama wanda ke ruguza shirye shiryensu kamar amfani da bama bamai ta hanyar tauraron dan adam da ke iya hango komai daga sama, kai bama haka ba ana iya hango komai dake saman kasa ta hanyar amfani da na’urorin zamani, wanda hakan ke kasancewa wani lamari ne da ya gagara su kalubalance shi.
Saboda haka kafofin yada labarai ke kasancewa mafaka wanda yake kiyayewa wadancan kungiyoyin wanzuwarsu da yaduwarsu, tare da samun daman horar da mutane da yawa domin shiga cikin kungiyoyinsu da kai musu hare hare.