Hakkokin masu bukatu na musamman.

Egypt's Dar Al-Ifta

Hakkokin masu bukatu na musamman.

Tambaya

Shin masu bukata ta musamman sun cancanci da a basu zakka?

Amsa

Wanda bai da abin da zai iya biyawa kansa bukata na ciyarwa ko kuma ciyar da wanda nauyinsa ke wuyansa kamar ciyarwa tufatarwa ko matsuguni da kulawa da lafiya ko ilimantarwa da sauran abubuwa makamantan haka, to ya halasta a ba shi zakkah har zuwa lokacin da zai samu daman tsayuwa da kansa, abin lura anan shi ne kallon halin da mutum ke ciki ba tare da la’akari da cewa shi yaro ne ko mai bukata ta musamman ko maraya, amma idan mutum ya kasance cikin wadanda aka ambata cikin fadin Allah Ta’ala : (Ita dai zakkah ana bayar da ita ne ga talakawa da miskinai da masu aikin amsa da rabawa da wadanda ake kokarin jan ra’ayinsu ga musulunci hakanan wanda ke zama bawa mukatibi da wandanda ake bin su bashi hakanan matafiya, wannan umurni ne daga Allah, domin Allah ya kasance mai hikima ne kuma masani) {Tauba:60} To ba a  baiwa mutum zakkah idan baya cikin jerin wadannan mutanen da aka ambata, ko da kuwa ya kasance shi mai bukata ta musamman ne.

Share this:

Related Fatwas