Karama da mu’ujiza.
Tambaya
Me ake nufi da karama? Ya iyakokinta suke? Mene ne bambancin dake tsakaninta da mu’ujiza?
Amsa
Ita karama dai aiki ne wanda ya sabawa al’ada wurin aukuwa, Allah ya na gudanar da shi ne ga wani bawa salihi, karama ba ta da alaka da da’awar annabta, ma’abocin karama ba ya da’awar annabta, domin hakan wani sashe ne na girman da Allah ke baiwa bayinsa salihai da waliyansa masu girma, kamar dai takura kasa garesu – nesa ta zama kusa – ko kuma sandararrun abubuwa su rinka yin tasbihi tare da su, da sauran abubuwan makamantar haka na karamu, wadanda aka saba gani daga waliyai, kamar dai yanda hakan ya gudana tare da sahabbai da tabi’ai, musamman nagartattun mutane na wannan al’umma, kaifinta – karama - shi ne gudanar abu wanda ya sabawa al’ada na faruwansa a zahiri ba wai na hankali ba, misali a bisa al’ada shi ne duk wanda ya shiga cikin ruwa shi ne ya nutse, Allah na iya girmama wani bawa daga cikin bayinsa da rashin nitsewa domin girmamashi da nuna nagartansa da waliccinsa sai ruwan ya dauke shi ba tare da ya nutse ba, a bisa al’ada wannan abu ne korarre, amma korarren abu na hankali ne shi ne yasa hankali ba zai iya tunanin faruwar hakan ba, kamar dai mutum ya samar da wani abu a cikin wani abu.
Bambancin da yake tsakanin karama da mu’ujiza shi ne, ita mu’ujiza al’amari ne wanda ya sabawa al’ada a wurin faruwansa wanda Allah yake gudanar da hakan a hannun wanda yake ikirarin Annabta domin gasgata ikirarinsa cewa shi manzon Allah ne daga Ubangijin talikai, ita kuma karama al’amari ne wanda ya sabawa al’ada wanda ba ya hade da ikirarin annabta, ya halasta ta bayyana ga wanda Allah ya so shi da hakan daga bayinsa gaba dayansu.