Isra’i da mi’iraji

Egypt's Dar Al-Ifta

Isra’i da mi’iraji

Tambaya

Mene ne hakikanin mu’ujizar isra’i da mi’iraji, kuma mene ne dalilin da ke nuna afkuwarsu, kuma mene ne hukuncin wanda bai yarda da su ba?

Amsa

Tafiyar Isra’i da Mi’iraji dai wani lamari ne da ya faru a zahiri ga shugabanmu Manzon Allah (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) kuma a fadake domin girmamawa daga Allah Ubangijinsa mai girma da buwaya, ta inda akayi tafiya da shi cikin dare a fadake daga masallacin Harami zuwa Masallacin Al’Aksa, inda anan ya yi sallah a cikin masallacin da Mala’iku da Annabawa – Allah ya kara musu aminci – sannan aka hau sama da shi  (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) a fadake daga Masallacin Al’Aksa zuwa sammai madaukaka, daga nan kuma sai zuwa kololuwar daukaka.

Anan ne aka bijiro ma da Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) cikin wannan daren mai albarka ayoyi masu girma, daga ciki akwai Aljannah, domin ya ga abubuwan da Allah ya tanazawa ma’abota cikinta, na daga lada da ni’imomi domin ya yi wa masu jin tsoron Allah albishir da ita, hakanan an bijiro masa da wuta domin yaga abin da ke cikinta na azaba mai radadi, domin ya yi kafiraida mushirikai gargadi da ita.  

Sannan Allah Ta’ala ya farlanta wa Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) da al’ummarsa – A cikin wannan daren mai albarka – salloli guda biyar da cikin yini da dare, wanda ladansu yakai na guda hamsin, inda Allah ya yi masa kyauta mai girma wanda babu wani cikin ‘yan’uwansa Annabawa da ya samu irin nasa Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam).

Hakika Alkur’ani Mai girma da Hadisai masu tsarki da taruwan sahabbai da sauran malamai sun tabbatar da cewa babu wani dalili na kin amincewa da faruwan Isra’i da Mi’iraji, ba wanda zai yi inkarin hakan sai karkatattu da masu dagawa.

Share this:

Related Fatwas