Shaye- shaye miyagun kwayoyi
Tambaya
Mene ne hukucin shan miyagun kwayoyi?
Amsa
Shan duk wani nau’i na miyagun kwayoyi haraumun ne; gaba dayan shari’a ta zo ne domin ta kiyaye hankali, da kuma ba shi kariya; bugu da kari kuma su wadannan miyagun kwayoyi sun kai wa zuwa ga cutarwa mai muni a lafiya da rayuwar zamantakewa. Shi kuwa sayar da su ya kai matakin manyan zunubai masu halakar da mai yinsu; domin mai sayar da su yana rusa al’umma da rayuwar al’umma ne, yana kuma cutar da al’umma da kasa ne baki daya.
Allah shi ne masani