Cinikayya ta hanyar biya kadan- kadan
Tambaya
Shin ya halatta a yi Cinikayya ta hanyar biya kadan- kadan, idan hajar ba ta hannun mai sayarwa?
Amsa
Hakinanin wannan mu’amalar ita ce “Cinikayyar murabaha”, wadda Imam al- Shafi’iy ya yi magana akanta a cikin littafinsa “al- Ummu”, yadda take kuwa shi ne: “Mutum ya nuna wa wani mutum haja, sannan ya ce masa: ka sayi wancan hajar, ni kuma zan b aka ribar kaza a kai”, cinikayyar murabaha da wannan surar abu ne da ya halatta, babu komai a ciki.