Amfani da karfi tsakanin iyalai
Tambaya
Mene ne hukuncin amfani da karfi tsakanin iyalai, musamman akan mata?
Amsa
Amfani da karfi tsakanin iyali abu ne mai muni a shari’ar Musulunci, haramcin haka yana kara girma musamman idan akan mace aka yi amfani da karfi, yakan fi tsanani idan akan mata ce, lallai shari’a ta gina harsashen mu’amala da mace akan soyayya da tausayi; saboda haka dukar matar aure, ko yin amfani da karfi akanta haramun ne; abin da ayar suratun Nisa’i ta ambata na duka, yana nufin wata sura ce ta tarbiyya da ta dace da wani sanannen yanayi, yana kuma da ka’idojinsa, da mutane suka manta shi da gangan har suka kai ga fitar da shi daga gwadaben manufarsa; saboda haka, babu laifi idan aka hana yinsa, aka mayar da shi ya zama laifi, daidai da sauyawar dokoki da rayuwar zamantakewa, sai hana shin ya zama shi ne ya yi daidai da aikin Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), da kuma manufofin shari’ar Musulunci masu tsarki, da dabi’unta.