Yanda ake tsara yin janaza.

Egypt's Dar Al-Ifta

Yanda ake tsara yin janaza.

Tambaya

Ta yaya ake tsara mamata domin yi musu sallah idan suka kasance maza ne da mata da yara kanana a hade?

Amsa

Idan janaza ta kasance ta kunshi mutane daban-daban, kamar ya zama akwai maza da mata da kuma kananan yara, to akan gabatar da mafificin cikinsu ne a gaba, kodai a sanya su daya bayan daya, anan sai a sanya mafi girman shekaru a gaba, ko kuma a sanya sashensu a bayan sashe, ko kuma a sanya su a jere, sai liman ya tsaya a tsakiyarsu domin ya yi musu sallah, a wurin addu’a kuma aka fadiwa mata kwatankwacin abinda ake fadawa maza ne.

Idan kuma suka kasance kananan yara ne maza da mata, sai a sanya yaran maza a kusa da liman, mata kuma a bayan mazan a bangaren alkibla.

Idan kuma janaza ta kunshi maza ne da mata: to abinda mazhabobin fikihu suka tafi akansa, kuma shine mafi bayyana daga magabata da jumhorin malamai, shine gabatar da maza zuwa bangaren liman, tare da sanya mata a bangaren alkibla, amma idan ya zama a cikin janazan akwai kananan yara. To sai a sanya su a bayan maza, sannan a sanya mata a bangaren alkibla.

Share this:

Related Fatwas