Ajiye kudade a bankuna
Tambaya
Mene ne hukuncin ajiye kudade a bankuna?
Amsa
Ajiye kudade a bankuna da amsar fa’idar da suka haifar abu ne halal, babu laifi a cikinsa, ba shi ne ake kira rib aba, hasali ma sabon tsari ne na yarjejeniya wanda ya yi daidai da manufofin shari’ar Musulunci wajen mu’amaloli a fikihun Musulunci, wanda kuma ana matukar bukatarsa, rashin sa yana tsayar da maslahohin mutane, ribar da bankuna suke bai wa abokin huldarsu riba ce da aka samu bayan an yi kasuwanci da kudaden da ya ajiye, an habaka yawansu, saboda haka ba wannan ne riba da aka haramta ba; saboda ba fa’ida da aka samar da su sakamakon bashi ba, ba kuma amfani ne da ya samu sakamakon yarjejeniya ta tabarru’i ba, hasali riba ce ta kudaden da ya sanya aka juya, inda suka samar da maslahohi ga bangarin mu’amalar.