Ribar bankuna.

Egypt's Dar Al-Ifta

Ribar bankuna.

Tambaya

Wasu dalilai ne suka halasta amfani da ribar da ake samu a bankuna?

Amsa

Hukumar bayar da fatawa ta kasar Masar ta tafi akan hukuncin halasta kudin da ake samu na ribar bankuna, - wannan fatawar ta dade sosai daga wannan hukuma- saboda wannan kudin riba ne da aka samu sakamakon yarjejeniya na ciniki da aka kulla, wanda dukkanin bangaroran da abin ya shafa suke amfana da ciniki da kuma ribar da aka samu, wannan yana tabbata ne saboda wasu dalilai masu zuwa kamar haka:

Na farko: ka’ida tana cewa: ya halasta a sabunta sababbin cinikayya, matukar babu garari da cutarwa a ciki, yarjeniyoyin bankuna su na daga cikin wadannan.

Na biyu: Wannan mas’alar ana iya ganin abin da ake iya amfana da shi, kamar gwamnatoci da kamfanoni da kuma daidaikun mutane, ta hanyar amfani da bankuna, domin bankuna sune kadai suke iya daidaita farashi da ribar kasuwanci da basuka a tsakanin mutane, sannan bankuna sune suke iya gaggauta samar da hanyoyin cigaba ta bangaren masana’antu da kasuwanni da sauran hada-hadan kasuwanci.

Na uku, kuma na karshe: Dokokin bankunan kasar Masar mai lamba 88 na shekara 2003, sannan an fara amfani da wannan doka a shekarar 2004, dokar ta bayyana cewa: alaka tsakanin banki da mai ajiya, kamar alakar zuba hannun jari ne da samar da hanyoyin samar da kudade; amma ba wai ba shi ba ne.

Share this:

Related Fatwas