Yin gargadi akan ha’inci da kuma wa...

Egypt's Dar Al-Ifta

Yin gargadi akan ha’inci da kuma warware alkawari

Tambaya

Ta yaya shari’a ta yi gardadi akan ha’inci da warware alkawari?

Amsa

Annabi SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam ya ambaci cewa shi dai ha’inci da warware alkawari dabi’ace daga cikin dabi’un munafukai, ya wajaba ga mumini ya tsarkaku daga hakan, an karbo daga Abdullahi bin Amr -  Allah ya kara musu yarda yace: Annabi SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam yace: Wasu halaye guda hudu, duk wanda ya yake da su to ya kasance cikakken munafiki, wadannan halayyar su ne: Idan ya yi magana sai ya yi karya,  idan ya dauki alkawari sai ya saba, idan aka kulla amana da shi sai ya yi ha’inci, idan aka yi fada da shi sai ya yi butulci, duk wanda yake da irin wadannan dabi’un to yana da dabi’un munafinci har sai ya rabu da su. Anyi ittifaki akan wannan hadisin.

Share this:

Related Fatwas