Yin amfani da kimiyyar kwayoyin hal...

Egypt's Dar Al-Ifta

Yin amfani da kimiyyar kwayoyin halitta wajen magani

Tambaya

Mene ne hukuncin yin amfani da kimiyyar kwayoyin halitta wajen yin magani?

Amsa

Kwayoyin halitta wasu kwayoyi ne da suke da ikon rarrabuwa da yawaita, su samar da wasu nau’o’in kwayoyin na musamman, da suke harhaduwa su samar da jikin na daban, malamai a wannan zamanin sun sami daman sanin wadannan kwayoyin, da kuma killace su, da ma kara yawansu; da niyya yin amfani da su wajen magance wasu cututtuka. Zai yiwu a iya samun wadannan kwayoyin ta jikin jarirai, a marhala ta farko ta halittar jariri, ko a lokacin da aka yi bari, ko a kowace marhala daga cikin marhalolin ciki, ko ta hanyar biyawar- uwa, ko ta igiyar cibiya, ko ta hanyar kananan yara, ko balagaggu, ko ta hanyar kwafi da daukan wasu kwayoyin halitta a cikin jiki.

Samun wadanan kwayoyin halitta, da kara yawaita su da amfani da su wajen magani, ko gudanar da bincike na ilimi da ya halatta, matukar dai ba su cutar da wanda aka debe su daga jikinsa ba, wannan ya halatta a shari’ance.

Bai halatta a debi kwayoyin halitta ta hanyar da shari’a ta haramta ba, kaman a janyo barin jariri da gangan, ba tare da wani dalili na shari’a ba, ko ta hanyar hada tsakanin kwayoyin maniyyin wata mata, da maniyyin wani namiji da ba muharraminta ba, ko a deba daga karamin yaro koda kuwa da izinin waliyyinsa; saboda waliyyi ba shi da hakkin ya yi tasarrufi akan abubuwan da ya kebanci wanda yake yi wa waliyyanta sai a abubuwan da za su dawo wa wanda ake yi wa waliyyantar da amfani tsantsa.

 

Share this:

Related Fatwas