Sauya niyya daga farali zuwa nafila...

Egypt's Dar Al-Ifta

Sauya niyya daga farali zuwa nafila, ko akasi

Tambaya

Sauya niyya daga farali zuwa nafila, ko akasi

Amsa

A shari’a kowa ya sani cewa halarto da niyya ana yinsa ne kafin a fara gabatar da aiki, niyya sharadi ne na ingancin sallah a wurin wasu daga cikin malaman fikihu, wasu kuma suka sanya ta a matsayin rukuni daga cikin rukunnan sallah, game da sauya ta a sallah kuwa, bai halatta a sauya daga farali zuwa wani faralin na daban ba, ko daga nafila zuwa farali, lallai wasu daga cikin malaman fikihu sun tafi akan cewa yin haka yana bata sallah tun daga asalinta, wasu kuma sun tafi akan cewa hakan zai iya sauya sallah daga farali ta koma nafila, amma game da sauya niyya daga farali zuwa nafila, ko daga nafila zuwa wata nafilar, wannan ya halatta idan an sami uzuri akan haka, lallai daukacin malamai sun hadu akan haka, wasu ma sun ce ya halatta koda babu wani uzuri.

Share this:

Related Fatwas