Lalacewar kayan sayarwa bayan an si...

Egypt's Dar Al-Ifta

Lalacewar kayan sayarwa bayan an siya an bari a wurin mai sayarwan sannan kayan ya bata.

Tambaya

Mene ne hukuncin kayan da aka saya aka biya kudinsa sannan aka bari ajiya a wurin mai sayarwa sannan kayan ya bata?

Amsa

Idan mutum ya sayi kaya bayyananne ya biya kudin kayan ya amsa, sannan kuma ya bari a wurin mai sayar da kayan ajiya domin ya kamala wasu bukatunsa, to anan akwai abubuwa guda biyu da ya kamata a sani:

Kulla ciniki ingantacce kuma cikakke da ya cika rukunai da sharuda, wanda ya kai ga mallakan mai saye ya zama nasa kuma a hannunsa, har ya zama yana da hakkin tasarrufi akansa.

Ajiyan kaya ba tare da biyan kudin gadi ba, wato ana nufin bayar da ajiyan dukiya a matsayin sadaka, kulla yarjejeniyar ajiya halastaccen abu ne a shari’a, kayan ajiya dai amana ne a hannun wanda aka ajiye kayan a wurinsa, domin shi amintacce ne, idan kayan suka bace ba zai biya ba, sai dai idan shine ya wofintar da kayan ko ya yi sakaci suka lalace ko suka bata, shin kayan sun bata ne ta yanda za a iya kiyayewa ne ko a a, sabanin wanda kayan suka bace a wurinsa bayan an biyashi kudin ajiya, to shi wannan idan har kayan su ka bata a yanayin da zai iya kiyayewa kamar sata, amma bai yi ba to zai biya, amma idan kayan suka bace a yanayin da ba za a iya kauce masa ba kamar mutuwa, to ba zai biya ba, amma idan suka yi yanjejeniya a tsakaninsu bayan batan kayan to babu laifi.

Share this:

Related Fatwas