Jinkiri wurin raba gado.
Tambaya
Mene ne hukuncin jinkirta raba gado sabanin bukatun magada?
Amsa
A duk sanda aka tabbatar da mutuwar wanda za a gada to duk mai gado ya cancanci rabonsa na abinda aka bari bayan cire abinda zai isa ayi masa sutura da kuma biyan basussukan da ake binsa, tare da bayar da wasiccin da yayi da kaffarorinsa da bakace ko makamancin haka.
Bai halasta ga kowa ba daga cikin magada ya katange sauran magada daga samun kasonsu na gado da aka yanke musu a shari’ance, ta hanyar hanashi ko nesantashi daga gadonsa, hakanan bai halasta a fifita wani cikin magada na yayi tasarrufi cikin dukiyar ba tare da sanin sauran ba ko ba tare da yardansu ba, hana rabon gado ko jinkirta rabawa ba tare da wani dalili ba ko amincewar magada to haramun ne a shari’ance saboda fadin SallallaHu AlaiHi wa AliHi wasallam: (Wanda ya nesanta magada daga gadonsu, to Allah zai nesanta “yanke” gadonsa daga Aljanna ranar Alkiyama) Ibn Majah a sunan dinsa, hakanan fadin SallallaHu AlaiHi wa AliHi wasallam: (Duk wanda ya yanke gadon da Allah ya farlantashi, to Allah zai yanke nasa gadon daga Aljannah).Baihaki.
Allah Ta’ala ne mafi sani.