Jinkirin raba gado.
Tambaya
Mene ne hukuncin jinkirta raba gado bayan mutuwa?
Amsa
Gado bayan mutuwar wanda aka gaba hakki nan a daukacin magada a tare –mazansu da matansu, manyansu da kananansu-, kowa daga cikinsu zai zama ya cancanci rabonsa a ciki, bayan an cire kudaden hidimar hada mamacin, bayan kuma an biya basussukan da ake binsa, an kuma zartar da wasicin da ya yi.
Sai bai halatta wani ya shiga ya fita ya zama cikas ga sauran magada na su sami rabonsu da shari’a ta raba ta ba su ba, shin ta hanyar hana su ne kwata- kwata, ko jan- kafa wajen raba gadon, haka ma bai halatta wani ya yi wani tasarrufi da gadon ba tare da sauran magada, ko izininsu ba, saboda haka hana rabawa, ko jinkirta rabawar ba tare da wani dalili ba abu ne da shari’a ta haramta, kuma maganar Allah Madaukakin Sarki ne yake tabbatar da haka, Allah y ace: (Ku kuma yi gaggawa zuwa ga gafarar da ta zo daga Ubangijinku, da aljannar da fadinta ya kai fadin sammai da kasa, duka an tattale ta ne saboda masu tsoron Allah) [Ali Imran: 133], a cikin wannan ayar akwai umurni da yin gaggawa zuwa ga duk wani abu da zai gadar da gafara, da shiga aljanna, kuma a cikin manyan hanyoyin samun shiga aljanna, da samun yardar Allah akwai bayar da hakkokin bayi.