Wasiyya wajiba
Tambaya
Mene ne hukuncin shari’a game da wasiyya wajiba?
Amsa
Wasiyya wajiba ita ce: wani kaso ne da ake fitarwa daga cikin dukiyar da mamaci ya bari, domin bayar da shi ga wadanda suka cancanta a matsayin wasiyya, inda doka ce ta wajabta haka, shin magada sun yarda ko ba su yard aba, ana bayar da ita ne ga ‘ya’yan magajin da ya rasu a lokacin da mahaifinsa yake raye, da sharadin kada ya zama suna da gado a asali, wajibi ne a fitar kafin a kai ga rabon gado.
Wajabta wasiyya wajiba da doka ta yi abu ne da shari’a ba ta hana ba; lallai wasu daga cikin tabi’ai da masana fikihu masu ijtihadi sun tabbatar da ita, irinsu: Imam al- Dabariy da Ibn Hazam, da Dawud, sun kuma dogara ne da maganar Allah Madaukakin sarki da yake cewa: (An wajabta maku cewa: a duk wanda mutuwa ta zo wa wani daga cikinku, matukar ya bar dukiya, to ya yi wasiyya ga iyaye biyu, da makusanta cikin kyautatawa, wannan hakki ne da yake akan masu tsoron Allah) [al- Bakra: 180], wannan kuwa saboda ayar muhakkama ce ba a share hukuncinta ba.
Babu laifin idan doka ta wajabta wani abu da yake ibada ne da sada zumunci da kuma maslahar da nassoshin shari’a ba su hana ba, hasali ma a ciki akwai abin da zai karfafa shi.