Wakilci na shari’a

Egypt's Dar Al-Ifta

Wakilci na shari’a

Tambaya

Mene ne hukuncin wakilta wani a wajen saye a kasuwancin da ake biyan kudinsa kadan- kadan?

Amsa

Babi laifi a wakilta wani ya sayi haja da sunan wani; idan mun yi la’akari da asalin hukuncin wakilci, wanda abu ne da ya halatta.

Amma a ce mai sayen hajar “wakilin” shi ne kuma mai sayarwa kansa bayan wakilci; to wannan mas’ala ce da take da sabani a tsakanin malaman fikihu, akwai maganganu guda biyu akai: abin da ake bayar da fatawa da shi shi ne halaccin wakili ya sayarwa kansa, idan wanda ake wakilta ya yi izini, amma idan bai yi izini ba, bai halatta ba, wannan shi ne hukunci a mazhabar Malikiyya da Hanbaliyya, kuma fuska daya ce daga cikin fuskokin hukunci a shafi’iyya, shi ne kuma abin da dokar kasuwanci mai lamba 17, ta shekarar 1999, wadda aka yi mata gyara da doka mai lamba 168 ta shekarar 2000, da doka mai lamba 150 ta shekara 2001, a doka mal lamba (156) suka yi aiki da shi.

Game da biyan kudin hajar da wakilin ya sayar wa kansa a rarrabe kadan- kadan, tare da ribar da aka yi ittifaki akansa kuwa, wannan abu ne da shari’a ba ta hana ba; saboda abin da ya tabbata a shari’a shi ne: ya halatta a sayer da haja da kudi hannu, ko da bashi zuwa wani sanannen lokaci, karin kudi akan biyan da aka jinkirta zuwa wani sanannen lokaci abu ne da shari’a ta halatta, kaman yanda jamhur din malamai masana fikihu suka tafi akai, domin hakan yana cikin babin murabaha ne.

Share this:

Related Fatwas