Horar da kananan yara mata akan sal...

Egypt's Dar Al-Ifta

Horar da kananan yara mata akan sallah

Tambaya

Shin ya halatta yara su yi sallah ba tare da alwalla, ko sanya hijabi ga mata ba domin horarwa?

Amsa

Horar da kananan yara -a gidaje da makarantu- game da yanda za su yi sallah, ta yanda zai dace da yanayin zai sanya su so ta, su kuma fuskance ta –koda ta hanyar da ba sai sun yi alwalla, ko kananan yara mata sun sanya hijabi ba- abu ne da mai yinsa yake samun lada, ina ma a ce wajen yin haka an nemi shawarwarin kwararru wajen sanin halayyar kananan yara, da masu aiki wajen gina tarbiyya a cikin zukata, tare da hakuri da kuma neman lada a wurin Allah akan horas da kananan yara akan yanda za su yi ibada, su kuma gabatar da ayyukan da addini ya wajabta masu, lallai a cikin yin haka akwai ma’anar hakurin da shari’a ta bayar da umurnin a yi a inda Allah Madaukakin sarki ya ce: (Ka umurci iyalanka da yin sallah, ka kuma yi hakuri da juriya wajen yin wannan umurni, ba za mu tambaye ka game da arziki ba, mu ne muke azurta ka, karshe mai kyau na masu tsoron Allah ne) [Taha: 132], da maganar Allah mai girma: (Ya kasance yana umurtar iyalansa da su yi sallah, su kuma bayar da zakka, lallai shi yardajje ne a wurin Ubangijinsa) [Maryam: 55].

Share this:

Related Fatwas