Gargadi game da murnar a mutuwa, da...

Egypt's Dar Al-Ifta

Gargadi game da murnar a mutuwa, da idan ibtila’i ya faru, da bayani akan sakamakonsa

Tambaya

Gargadi game da murnar a mutuwa, da idan ibtila’i ya faru, da bayani akan sakamakonsa

Amsa

Sam bai halatta mutum ya yi wa dan uwansa dariya a lokacin da ibtila’i na mutuwa, ko wanin mutuwa ya faru da shi ba; lallai wannan mummunar dabi’a ce, zukatan da suka akan kyakkyawar hanya suna kyamatar haka, masu mutunci suna nesantarsa, saboda haka ne shari’a ta hana, an ruwaito Hadisi daga Wasilat Bn al- Asqa’i (Allah ya kara yarda da shi) cewa manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Kada ka bayyana murna da ibtila’in da ya sami dan uwanka, sai Allah ya kubutar da shi, kai kuma ya jarrabe ka) [al- Tirmiziy], mu a nan muna kara tunatar da wadanda suke da wannan mummunar tada da cewa: lallai sunnar Allah ta tabbatar da cewa dan Adam ba ya zama akan hali guda daya, lallai yana rayuwa ne wata rana cikin farin ciki, wata rana kuma cikin bakin ciki, Allah mai girma ya ce: (Idan wani miki ya same ku a yau, to ku sani cewa lallai irin wannan mikin ma ya sami wasu mutane irinku, lallai wadannan kwanaki ne da muke jujjuya su a tsakanin mutane..) [Ali Imran: 140]. A cikin abin da aka ambata akwai amsar tambayar.

Share this:

Related Fatwas