Bayani game da abin da Hadisin: “Sa...

Egypt's Dar Al-Ifta

Bayani game da abin da Hadisin: “Sallah a lokacinta” yake nufi.

Tambaya

Mene ne ma’anar Hadisin: “Fiyayyen ayyuka shi ne sallah a lokacinta”?

Amsa

An ruwaito Hadisi daga Ibn Mas’ud (Allah ya kara yarda da shi), cewa wani mutum ya tambayi Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) cewa: wane aiki ne ya fi falala? Sai ya ce: (Sallah a lokacinta, da bin iyaye, sannan jihadi akan hanyar Allah) [al- Bukhari].

Wannan Hadisi ba ya nuni zuwa ga wajibcin yin sallah a farkon lokaci; domin kawo kalmar “abin da ya fi” yana nufi duka biyun suna da falala, kawai dai daya ya fi daya ne; karshen abin da ake nufi shi ne yin sallah a farkon lokaci ya fi falala, matukar wani abu mai bijirowa bai bijiro wa wannan falalar ba, sannan wannan Hadisi ya ambaci sallah a lokacinta, ba tare da ya ayyana farkon lokacin da yake da wannan falalar ba; Imam Ibn Dakikil Edi a cikin littafinsa “Ihkamul Ahkam” [1/163] ya ce: “A cikinsa babu abin da ya bayyana farkon lokacin da karshensa, manufarsa ita ce: togaciya da sallar da aka yi ta a wajen lokacinta na kada’i”.

Share this:

Related Fatwas