Hada salloli wuri daya
Tambaya
Mene ne hukuncin hada salloli wuri daya saboda saukan ruwan sama?
Amsa
Abu na asali dai shi ne wajabcin tsayar da sallah a lokcinta ba tare da jinkiri ko gaggautawa ba, Allah Ta’ala ya ce: (Lallai ita sallah ta kasance abin wajabtawa de na lokaci ga muminai) {Nisa’i:103}.
Hada salloli wuri daya yana kasancewa ne kadai a yanayi na togaciya, kuma hakan baya kasancewa sai da uzuri, daga cikin uzururrukan da suke sanyawa a hada salloli wuri daya a lokaci daya, daga ciki akwai saukan ruwan sama mai tsanani, wanda zai tsananta wurin tafiya zuwa masallaci, ta inda komawa zuwa yin sallar la’asar bayan azahar zai yi wuya, ko kuma komawa zuwa yin sallar issha’i bayan sallar magariba zai tsananta.
To abin da aka tsaya akai na fatawa a wannan yanayin shi ne halasta hada sallolin biyu a lolaci daya, kamar azahar da la’asar, da kuma magariba da issha’i, anayi ne a lokacin sallar farko, ba tare da yin kasaru ba, domin ya zo a “sahihaini” an karbo daga Abbas Allah ya kara masa yarda ya ce: Annabi SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam ya yi sallar azahar da la’asar atare, haka nan ya sallaci magariba da issha’i a hade a Madina, Imam Muslim ya kara da “ba tare da kasancewa cikin yanayin tsoro ba kuma ba a yanayin tafiya ba” Imamu Malik da Shafi’i Allah ya yi musu rahama sun ce: “suna ganin dalilin hada sallolin bisa dalilin ruwan sama ne”.