Hada salloli a lokaci daya.
Tambaya
Shin ya halasta a hada salloli fiye da daya a lokaci daya saboda uzuri?
Amsa
Asalin yin sallah na farilla shine gudanarwa a lokacinta, wanda hakan yana daga cikin ayyuka mafi soyuwa ga Allah Ta’ala.
Saukaka hada salloli biyu lokaci daya kamar azahar da la’asar, ko magariba da Issha’i saboda rashin lafiya ko tafiya to abu ne wanda yake halas bisa ittifakin jumhorin malamai.
Hada salloli biyu a lokaci daya bisa uzuri kamar dai gudanar da wata bukata ko shagaltuwa da wani aiki ko makamancin haka, to lamari ne wanda ya halasta a shari’ance, amma da sharadin kar hakan ya zama koda yaushe.
Tare da kiyayewar mai hada sallar na yin niyyar hada sallar wuri daya a lokaci na farko idan ya yi niyyar hadawa a lokacin farko, ko kuma ya yi niyyar jinkirtawa, idan mutum yayi haramar yin sallar a loakcin na farko ko a yayin gudanarwa idan yayi niyyar gaggautawa, kuma kar ya zama akwai tazara mai yawa tsakanin sallolin guda biyu.